<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Yaƙi 'Na Nan, Yaƙi Na Almasihu Ne LW281</title>
<lyrics>[V1]
 1) Yaƙi 'na nan, yaƙi na Almasihu ne,
 Ku Masu Bi, yi shirin yaƙin nan.
 Ubangijinmu shi ne sarkin yaƙin nan
 Da mu ke yi, zai ba mu nasara.

[V2]
 KORUS
 Yaƙi 'na nan, ku Masu Binsa,
 Ku nemo kayan yaƙin nan,
 Sulken adalci, kwalkwalin ceto,
 Da garkuwa ta bangaskiya,
 Takalma na shirin bishara,
 Gaskiya ce ɗamararmu,
 Takobin Ruhu--Maganar Allah,
 Da su mu ke yin nasara.

[V3]
 2) Ku ƙarfafa a cikin Ubangijinmu,
 Ku tsaya fa ta wurin bangaskiya.
 Kokawarmu tare da Shaiɗan ne da
 Ikoki nasa da kuma zunubi.
 Korus

[V4]
 3) Ku yi aniya, ga Yesu yana zuwa
 Don ya dube mu a cikin yaƙin nan.
 Ga shi, hakkinsa yana nan tare da shi,
 Zai bayar wa masu cin nasara.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>281</hymn_number>
</song>